Shin ka san cewa a na samun kuɗi a yanar gizo? Ƙwarai da gaske, za ka iya samun maƙudan kuɗaɗe ta hanyar manhajan sada zumuntan da ka ke amfani da su a yau da kullum, irin su Tiktok, Facebook, Twitter, da dai sauran su idan har ka iya allon ka. Kamar yadda a ke samun kudi a Facebook, haka shi ma a ke samun kudi a Tiktok. A wannan maƙalar, zan yi ma bayanin yadda ake samun kudi a Tiktok daki-daki.
Manhajar TikTok
Tiktok wani dandali ne na sada zumunta wanda a ke wallafa bidiyoyi gajeru na nishaɗi.
An ƙaddamar da TikTok ne a watan Satumban shekarar 2016.
A shekarar 2017, manhajar ya canja suna Tiktok da a ka fi sani yanzu.
TikTok ya yi ƙaurin suna musamman lokacin kullen cutan Korona da mutane ba su da abin yi domin kuwa kamfanin Cloudfare ta ayyana su a matsayin shafin yanar gizon da ya fi kowane tashe har fiye da ma Google a 2021.
A Satumban 2021, ne Tiktok ya zarce masu amfani da mutum biliyan ɗaya.
A yanzu dai kam manhajar Tiktok shi ne Manhaja na shida a duniya, wajen yawan masu amfani, bayan Facebook, Youtube, Whatsapp, Instagram da Wechat.
Mutane da dama, musamman matasa na amfani da Tiktok domin yin rawa, waƙa, wasan kwaikayo, bada dariya, tallace-tallace, girke-grike da dai sauran su.
Hakan ya sa ya shahara, kuma bai kamata a ce ka na amfani da manhajar ba ka san yadda ake samun kudi a Tiktok ɗin ba.
Yadda Ake Samun Kudi A Tiktok
Idan ka na neman yadda ake samun kudi a Tiktok, sai mu ce ma akwai hanyoyi da yawa kuma sauki gare su kaman bude sabon gmail.
Duk da dai lokaci ba zai bari mu kawo duka ba, amma ga wasu daga ciki;
1. Affiliate Marketing
Affiliate marketing na ɗaya daga cikin yadda ake samun kudi a TikTok.
Affiliate marketing na nufin yi ma kamfanoni ko wasu daban talla, kai kuma sai ka samu wani kaso daga ciki.
Hakan na nufin idan har ka na da mabiya da yawa a Tiktok, da zarar ka tallata ma mabiyan wani samfuri kuma a ka saya, za ka samu kwamasho daga ciki.
Za ka iya shiga irin wannan tsarin da su Jumia, Amazon, Konga da dai sauran su.
Da zarar ka yi rajista, za a ba ka wani mahaɗar yanar gizo na musamman da ba mai irin ta.
Wannan ne za a yi amfani da shi a duba waɗanda su ka sayi kayayyaki ta dalilin ka, kuma har a samu daman biyan ka.
2. Gyarawa da Feƙe Bidiyo
Kafin yin la’akari da wannan hanyar a matsayin yadda ake samun kudi a Tiktok, ya kamata ku sami ɗan gogewa game da da gyaran bidiyo.
Da wannan ƙwarewar, za ku iya taimakawa masu ƙirƙira TikTok wajen gyara bidiyon su, saka masu abubuwa kamar su; effects, transitions, animations da dai sauransu.
3. Buɗe Asusun Tiktok Domin Sayarwa
Idan kun san yadda ake gina asusun TikTok kuma ku samu mabiya, to za ku iya amfani da wannan hanyar samun kudin a Tiktok.
Akwai mutane masu kasuwanci da ke buƙatan asusun Tiktok da su ka zarce mabiya 1000, domin inganta kasuwancin su.
Za ku iya sayar da asusun TikTok a kan farashi daga Naira dubu ashirin har fiye da dubu ɗari biyu. Hakan ya danganta da yawan mabiyan da ka tara.
Amma fa a kula, Tiktok kamar sauran kafafen sada zumunta ba su aminta da wannan hanyan ba, kuma za su iya dakatar da asusun na ka da zarar sun gano ka saɓa ma dokokin gudanarwan su.
4. Hanyar Tiktok Creativity Program
Za ku iya amfani da wannan hanyan ta Tiktok Creativity Program a Tiktok ke biyan masu ƙirƙiran bidiyo domin samun kuɗi cikin sauƙi.
Wani hanzari ba gudu ba, ku na buƙatar ku cika ƙa’idoji kamar haka, kafin samun daman shiga tsarin yadda ake samun kudi a Tiktok;
- Ka zarce shekaru 18
- Ka na da mabiya sama da 10000 (dubu goma)
- Ka samu masu kallon bidiyoyin ka guda 100,000 (dubu ɗari) a kwanki 30 da su ka gabata
- Amincewa da dokokin gudanarwa na Tiktok
- Ka kasance zaune a Amurka
Duk da dai wannan hanyar samun kudin a Tiktok ba ta samu ba ga mutanen Afrika ba tukuna, ya na da kyau ka zama cikin shiri kuma ka cika duk ƙa’idojin da a ke buƙata tun kafin a nema domin kuwa wannan hanya ce mai ɗorewa, kamar yadda mutane ke samun kuɗi a Youtube.
Karanta: Yadda Ake Bude Youtube Channel
Idan kuwa kai mazaunin ɗaya daga cikin ƙasashen da a ke biyan masu ƙirƙiran bidiyo ne ta wannan hanya, sai mu ce ma a nemu kuɗi lafiya.
5. Yadda Ake Samun Kudi a Tiktok; Yin Talla A Tiktok
Kamar yadda manyan masu shafuka a Instagram, Facebook, Twitter da ma sauran shafukan sada zumunta domin yi ma wasu talla, kai ma za ka iya amfani da wannan hanyar domin shiga tsarin yadda ake samun kudi a Tiktok.
Don haka za ku iya yin dabaru domin tallata samfuran wasu a cikin bidiyoyin ku.
Za ku iya taimakawa kamfanoni da masana’antun da ke son tallata samfuran su a kan Tiktok amma ba su da masaniya a kai.
6. Aiki A Matsayin Manajan Tiktok Na Wasu
Za ka iya kasancewa manajan wasu ƴan Tiktok da ba su da lokaci, ko kuma ka zama wakilin su a wurin kamfanoni, masu san yin talla da sauran su.
Hakazalika za ka iya zama mai sarrafa masu asusun su.
Kafin ka yi amfani da wannan hanyan wajen sanin yadda ake samun kudi a Tiktok kuwa, ka na buƙatar ka san yadda Tiktok ya ke aiki, ko kuma ya zama ka na da ilmin kasuwancin ko kuma kula da shafin sada zumunta.
7. Samun Kyautan Tiktok Coins
A matsayin ka na mai ƙirƙiran bidiyo, za ka iya samun kyautan Tiktok coins.
Masu amfani da manhajan su na sayen waɗannan coins ɗin da kuɗin gaske domin su yi kyautan su ga masoyan su.
Coins | Farashi a Dala |
500 coins | $6.49 |
1000 coins | $12.98 |
2000 coins | $26.99 |
5000 coins | $66.99 |
1000 coins | $134.99 |
Akwai kuma coins iri-iri kamar yadda za ku gani a cikin hoton nan, kuma kowanne kuɗin sa daban.

Har ila yau, za kuma ka iya samun kyautan Tiktok diamonds a yayin da ka ke Tiktok Live, wata watsa bidiyo kai tsaye.
Masoya za su iya turo ma wannan kyauta ta hanyan latsa madannin ‘gift’ a lokacin da ka ke kan yin shi ɗin, idan dai har sun saye su a da can.
Kammalawa
Duk da na yi iya bakin ƙoƙari na wajan yin bayanin yadda ake samun kudi a Tiktok, hakan ba ya nufin iya hanyoyin kenan.
Za ka iya saida kayayyaki, neman kyauta daga mabiya, ko kuma saka talla a bidiyoyin ka da kuma haɗa Tiktok ɗin da wani wurin da ka ke kasuwancin ka kamar su Facebook, ko Youtube da dai sauran su.
Ya na da kyau ka sani, kafin ka samu daman samun kudi a tiktok, ka na buƙatar tara magoya baya masu ɗimbin yawa.
Idan har ka na sha’awan sanin yadda ake samun kudi a Tiktok, wataƙila zai fi kyau ka fara sanin yadda za ka tara mabiya a Tiktok ɗin, daga nan komai zai zo cikin sauƙi.
Idan har ka yaba da wannan rubutun, to lallai ya kamata ka tura ma sauran ma’abota Tiktok domin su ma su amfana, a samu a gudu tare a kuma tsira tare.