Yadda Ake Samun Kudi A Facebook

Yadda ake samun kudi a Facebook

Shin ka san yadda ake samun Kudi a Facebook kuwa? Shin ka na sane da miliyoyin kudin da ake samu a Facebook? Idan har ba ka sani ba, to sha kuruminka ka biyo ni domin kuwa a wannan maƙalar zan bayyana ma ka hanyoyin yadda ake samun kudi a Facebook.

Facebook dai na ɗaya daga cikin manyan kafafen sada zumunta a duniya, in ma ba shi ne mafi girma ba. Facebook, wanda kamfanin Meta ta mallaka, Mark Zuckeberg da wasu tsirarun mutane su ka kafa shi a shekaran 2004.

A yanzu haka dai Facebook ya buwaya, domin kuwa mutane kusan biliyan 3 ne ke ziyartar su duk wata, wato kusan kaso fiye da 35 na gaba ɗaya mutanen duniya kenan. Akwai hanyoyin samun kuɗi da yawa a manhajan, da bai kamata a ce ka na kashe lokaci, da kuɗi ba tare da ka maida wani abu ba. Ba sai na cika ku da dogon bayanai ba, ga dai yadda ake samun kuɗi a Facebook.

Yadda Ake Samun Kudi A Facebook (Hanyoyi)

Na farko dai kafin ka san yadda ake samun kudi a Facebook, akwai wasu sharuɗan da za ka cika idan har ka na son samun kuɗi a Facebook. Bugu da ƙari, dandalin sada zumuntan ya na da jerin dokoki da ƙa’idoji waɗanda ke tsara yadda membobin za su iya samun kuɗin.

Ya kamata kuma ka sani cewa, akwai hanyoyin da ake bi wajen samun kuɗin da yawa a Facebook. Misali, za ka iya samun kuɗin shiga ta hanyar rukuni ko shafi akan dandamali. Ga dai bayanan filla-filla.

1. Hanya Na Farko: Facebook Stars

Facebook Stars wani tsari ne da facebook ke baiwa mutun damar samun kuɗi daga wajen mabiyan sa. Mabiyan na sa ko ‘Followers’ din za su iya siyan “Stars” su tura ma sa a a duk wani abin da a ka wanda akwai damar hakan, wato a ka yi ‘Enabling din Stars’.

Abin da ka wallafa ɗin zai iya kasancewa bidiyo ne, ko hoto, ko rubutu ne zalla kai ko ma bidiyon kai tsaye ne (live video).

Nawa ne duk star ɗaya a Facebook?

Kowane Star da mutum ya samu, Facebook za ta biyashi $0.01 USD wanda ya yi dai dai da Naira 9 a lokacin da a ka yi wannan rubutun.

Shin kowa ne zai iya amfani da Facebook star?

Idan kai ma’abocin yin bidiyon kai tsaye ne wato Facebook Live, to ya kamata ka ci gajyar wannan hanyan don sanin yadda za ka samu kudi a Facebook ta sanadiyan Facebook live ɗin na ka.

Sai dai fa wani hanzari ba gudu ba, ba kowa ne Facebook su ka baiwa daman shiga wannan tsarin ba, sai wanda ke gudanar da shafi a ƙarƙashin ‘Professional Mode’, wato tsarin gudanarwa na masana harkan kula da shafi a yanar gizo. Hakan kuma bai taƙaita da masu shafi a Facebook ɗin ba kawai, hatta karan ka da ka ke da akawun na ka na kan ka, za ka iya shiga wannan tsari.

Abubuwan da kawai ka ke buƙata sun haɗa da;

Yadda Ake Samun Kudi a Facebook – Hanya na Biyu

Bayan amfani da Facebook stars, hanya na biyu wajen samun kudi a Facebook shi ne ta hanyan kasuwanci a kan Facebook ɗin. Shi ne kuma mafi sauƙi wajen samun kuɗi hankali kwance a Facebook ɗin. Hasali, Facebook ya na bada damar siyar da abubuwa a wani sashe na musamman na shafin da a ke kira Facebook Marketplace.

A Facebook Marketplace, za ka iya gwanjon tsofaffin abubuwa, ko kuma ka tallata sababbi kuma a biya ka ƴan kwabban ka.

Yadda Za Ka Shiga Tsarin Facebook Marketplace

Ba kaman tsarin Facebook stars ba, Facebook Marketplace na da sauƙin sha’ani da kuma rashin matsi. Domin kuwa ƙa’idojin da a ke buƙata guda uku ne kacal, kuma sun haɗa da;

  • Kasancewa aƙalla shekaru 18
  • Ka mallaki akawun na Facebook da ya yi aƙalla kwanaki 30
  • Ka na zaune a ƙasar da a ka yadda da tsarin Marketplace.

Abin farin ciki shi ne, Najeriya na ɗaya daga cikin jerin ƙasashe 200 da ka yarda su yi wannan tsarin, don haka za ka iya saye da sayarwa a shafin ka. Za ka iya biyo mu a namu shafin na Facebook domin mu taya ka tallata hajar ka.

Ya na kuma da kyau wajen saida kayayyakin na ka, ka yi la’akari da waɗannan domin cin moriyan samun kuɗi a Facebook ɗin;

1. Tabbatar kun haɗa da bayyanannun hotuna na abin da kuke siyarwa.

2. Bayar da cikakkun bayanai kamar lambar waya, yanayin kaya, farashi da dai sauran su domin taimaka ma mai saye yanke hukunci.

3. Tabbatar da cewa ka farashin na ka akwai rahusa, ba ka tsula kuɗi ba.

Kula: Yayin da ka ke ƙoƙarin amfani da wannan hanyar domin samun kudi a Facebook, ya na da kyau ka yi la’akari da cewa ba lallai ba ne hakan ya zama kasuwanci na cikakken lokaci a kan Facebook ɗin ba, amma hanya ce mai sauri don samun ƙarin kuɗi.

Yadda Ake Samun Kudi A Facebook – Hanya Na Uku

Wataƙila kun lura cewa wasu mashahurai, ‘yan siyasa, malamai, yan kasuwa, kamfanoni da ma sauran manyan mutane su na amfani da Facebook sosai, don sanar da masoyan su halin da su ke ciki. Mafi yawanci kuma ba su da lokacin yin wannan da kan su. Saboda wannan ne su ke ɗaukan hayan masu kula da shafin su a kullum.

Daya daga cikin manyan shafukan Facebook a Najeriya.

Hakazalika kuma kamfanoni masu neman yin ciniki su ma su na amfani da kafan Facebook domin yin talla. Wannan ne dalilin da ya sa su ke da yawa ke ɗaukar masana domin tallata hajan su a Facebook.

Don haka, idan har ku na neman yadda za a samu kudi a Facebook ne, to za ku iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan ƙwararrun waɗanda za su iya taimakawa kasuwanci ta hanyar tara mabiya a Facebook da kuma sauyo mabiyan baya zuwa abokan ciniki, yin talla, ko kuma kula ma su da shafin.

Meyasa Zan Buɗe Asusu A Facebook?

Facebook wata hanyar sada zumunta ce a kafar sadarwar zamani ta yanar gizo. Facebook na bada damar haɗuwa da sababbin mutane, hulɗa da abokai da dangi, da kuma nishaɗi. Sai dai kuma da saura.

Karanta: Yadda Ake Bude Youtube Channel

Facebook na iya zama hanyan samun kuɗin ka ta yanar gizo, musamman idan ka na da mabiya da yawa kuma ka iya sarrafa shi yadda ya dace. Aa taƙaice dai, za ka iya tara maƙudan kudi a Facebook, idan har ka cancanta.

Idan kuwa ka na neman yadda ake samun kudi a Facebook ne, wanda kusan hanya ɗaya ne da yadda ake samun kuɗi a Tiktok, sai mu ce ka karanta bayanan da a ka yi a sama. Lallai kar ka bari a bar ka a baya.

Kammalawa

Facebook na da biliyoyin mutane da su ke ziyartar sa kullum, kuma mutane na amfani da shi don neman kuɗi. Da zarar ka fahimci yadda ake samun kudi a Facebook, kai ma kuwa za ka iya shiga sahun su.

Idan ka ji daɗin wannan rubutun, to ka yaɗa shi ga sauran masu sha’awar sanin yadda ake samun kuɗi ta Facebook domin a gudu tare a tsira tare.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply