Watan Ramadan lokaci mai muhimmanci ne ga musulmai a fadin duniya baki daya, musamman a Najeriya. Watan, wanda shi ne wata na tara a tsarin watannin musulunci, ana azumtar shi ne gaba-daya. To amma kafin a fara azumin, akwai niyya da ake yi. Wannan niyya, na da muhimmanci kwarai sosai, domin kaman yanda hadisi ya tabbatar, ba aikin da ya ke karbuwa a musulunci sai da niyya. To ya ake yin niyyan watan Ramadan? Akwai wata addu’a da ake yi ne na musamman, ko akwai wani abu da ake ƙudurcewa a zuciya?
Wannan rubutun zai bayyana ma ku yadda ake niyyar azumin Ramadan. Ga yanda bayanin ya ke.
Niyyar Azumin Ramadan
Azumin watan Ramadan ya na da muhimmanci ƙwarai a muslunci, domin hasali ma shi ne ginshiƙi na uku a musuluncin, bayan kalmar shahada da kuma sallah.
Hakan ne ya ja a na bukatan yin kyakkyawan niyya kafin fara Ibadan, duba da cewa wata daya za a shafe a na yi, domin gudun shan ƙishirwa kawai ba tare da samun lada ba.
Yadda Ake Niyyar Azumin Ramadan
Kaman yanda fitaccen malamin musulunci, Marigayi Muhammad Auwal Albani Zaria ya fada a wani karatun shi, abin da ake nufi da niyya shi ne tantance ayyuka da kuma samun ikhlasi.
To ya ake ake niyyar azumin Ramadan?
Malamai sun bada fatawa cewa lallai mutum yakan iya ɗaukan niyyan azumin watan ramadana ne, ana gobe za a fara azumi.
Wannan niyyan za a yi ta ne, ta game duka watan gaba daya, wato dai niyyan azumtar azumin watan gaba daya kenan. Malamai sun cire wannan hukuncin ne daga aya ta 185 a suratul baqarah na Al-qur’ani mai girma.
Idan kuma mutum na da tabbacin zai iya tashi kafin al-fijr ya keto, to lallai zai iya bari sai ya tashi yin sahur sai ya kudurce wannan niyyan a zuciyansa.
Idan an fahimta kenan, babu wata niyya da ake furtawa da baki, Kaman misali mutum ya fadi cewa ;
“na yi niyyan yin azumin watan ramadanan shekarar da mu ke ciki a waje kaza…”
To amma fa wani hanzari ba gudu ba.
Idan aka samu akasi ka kamu da rashin lafiya har ka sha azumi ko daya ne, to lallai sai ka sake sabunta wannan niyyan azumin ramadanan naka.
Hakan na nufin kowani rana sai ka yi ma ta niyyar ta na musamman, domin watan yanzu ya tashi daga matsayin abu daya ya koma kwanaki daban-daban wanda kowanne ke bukatar niyyar ta ta daban.
A taikace dai idan mun fahimta, mutum zai iya yin niyyan azumtar duka watan ramadana a daren da ake tsammanin ganin wata. Idan kuwa rashin lafiya ko wani uzuri ta sa aka sha azumi ko da daya ne, to kullum sai an sabunta yin wannan niya.
To tambaya a nan ita ce; ina hukuncin wanda ya kwana bai yi niyya ba amma ya tashi ya ga an ga wata? Malamai sun ma irin wannan mutumi uzuri, akan cewa lallai zai iya daukan niyan azuminsa da rana tsaka. Amma fa duk wanda ya ki kwana da niyyan yin azumin tun cikin dare da gangan, kuma ya farka alfijr ya keto, to shi aiki ya same shi. Malamai su ka ce shi sai dai ya kama bakinsa, domin bai da azumin wannan yinin.
A karshe, azumin watan ramadana ibada ne muhimmi da ake fatan musulmi ya samu karin kusanci zuwa ga Allah Madaukakin Sarki ta hanyan yin ibadoji kaman azumin, salloli na nafila irinsu tarawih da tahajjud, sadaka, zikiri, karatun alkurani, halartar majalisan tafsiri da dai sauransu. Da fatan za ku yi amfani da bayanin yadda ake niyyar azumin ramadan da kyau.
Allah Ya sada mu da alheran da ke cikin wannan watan, amin. Da fatan za ku cigaba da bibiyar shafin majalisarmu.