Yadda Ake Hawan Sallah A Kano

Yadda ake hawan sallah a Kano

Hawan Sallah na daya daga cikin shagulgulan da ake yi lokacin bukukuwan sallan idi a Kasar Hausa. A cikin garuruwan da ake yin hawan sallah a Arewa, wanda su ka hada da Daura, Zazzau, Katsina, Hadejia, Gumel, Sakkwato, Dutse, Kazaure, Bauchi, da dai sauransu, babu hawan sallah da fi ƙayatarwa fiye da na Kano.

Dalili kuwa shi ne, duk da cewa sauran garuruwa su na da na su bikin masu jan hankali, hawan sallah a kano yakan dauki wani salo na daban domin kuwa shi ne Hawan sallan da ya fi kowane kayatarwa da kuma shahara a duniya.

A Kano ne za ka ga mahaya dawakai cikin kayayyaki masu alfarma da kwalliya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano. To amma wataƙila kawai ganin wannan hawan ka ke yi a hotuna da shafukan zumunta, amma ba ka san yanda ake hawan sallah a Kano ba dalla-dalla.

To kar ka damu, domin kuwa kakar ka ta yanke saƙa. A wannan rubutun, zan bayyana maka yanda ake hawan sallah a Kano, tun daga sanda aka hau doki a ranan farko, har zuwa rana na ƙarshe. Ga yadda abin ya ke.

Ranar Farko: Hawan Sarki

Sarkin Kano shi ma zai fito, sanye da fararen kaya da alkyabba na alfarma kafin ƙarfe takwas na safe. Sarkin zai tako ne a ƙasa daga fadarsa, zuwa filin idin Kofar Mata. Sarkin zai iso ne a cikin minti talatin ko ƙasa da haka. Su kuwa Hakimai, su na take mai baya akan dawakansu.

Yadda ake hawan sallan idi a Kano
Sarki a hanyarsa na zuwa masallacin idi Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Sarki na isowa zai tarar jama’ar gari, babban limami, Gwamna ko wakilinshi su na jira. Zuwansa ke da wuya kuwa, za a tada salla.

Bayan idar da sallan, liman zai yi huduba da hausa da kuma larabci, ya kuma gargadi masallata. Daga nan fa Gwamna zai zo ya kawo camfa ga Sarki, tare da muƙarrabansa. Ana gama wannan kuwa, Makaman Kano zai ja tawagar mahayan, sai Kofar Wambai.

Daga nan za su wuce Zage, Sharifai, Yola, Satatima, su biya ta Kurawa kafin su ci birki a Fadar Sarkin wato Gidan Rumfa. A duk wuraren nan, Mai Martaba yakan karbi gaisuwa daga wurin talakawansa da su ka fito kallonsa da kuma yi masa fatan alheri.

Mai Martaba yakan tsaya wurin wasu dattawa musamman a Unguwar Sharifai, wanda jikokin Manzon Allah ne (S.A.W), su yi mai addu’a da kuma fatan tsawon rai.

Wannan addu’ar Sarkin Sharifai ko kum Sidi Fari, wanda jikan Abd al-Karim al-Maghili ne, babban malamin da ya tsara tsarin sarauta a lokacin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa.

Hawan Sallah a Kano

Daga nan fa Sarki zai nufi anguwannin Kofar Wambai, Dukawa, Darma da Zage, wanda su ka shahara da aikin fatu da jima lokacin mulkin mallaka ya karbi caffa.

Daga nan Mai Martaba zai wuce unguwar Satatima, sannan Kurawa inda yawancin masu sarautan garin su ke. Daga nan Sarki zai wuce, Gidan Shatima, wanda bawan Sarki ne lokacin Turawa, kuma aka maida shi gidansu. A yanzu kuwa, a nan Majalisar Sarki ta ke.

A nan ne Sarki za su gaisa da Mai Girma Gwamnan Kano da tawagarsa, da su ka hada da ‘yan majalisar zartarwa, kakakin majalisar jiha, Alkalin Jiha, da dai sauransu, ƙarƙashin mai masaukin baƙi Shugaban ƙaramar hukumar cikin gari.

Jawabin Sarkin Kano Ranan Hawan Salla

Bayan wannan, Sarki zai wuce Kofar Kwaru, wanda ke arewa da fadar kuma ta yi yamma da Unguwannin Kabar da Manadawari.

A nan ne Mai Martaba zai tsaya akan dokinsa, ya karbi gaisuwa daga Hakimai da kuma masu sarauta, daya bayan daya. Bayan nan Mai Martaba zai yi jawabin Salla zuwa ga talakawansa.

Rana Ta Biyu: Hawan Daushe

Ana yin hawan daushe ne a rana ta biyu na hawan sallah a Kano.

Yanda masana su ka tabbatar, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara wannan hawan, domin bawansa mai suna Daushe wanda bai samu halartar hawan salla ba.

Daga baya kuma, Sarki na yin wannan hawan ne zuwa gaida Mai Babban Daki, wato mahaifiyarsa.

Sarkin ya na fitowa ne daga Kofar Kwaru, ya bi ta unguwar Kabara, zuwa Tudun Wizirchi har ya ƙaraso fadar mai babban dakin a Gwangwazo.

Bayan rasuwan Mai Babban Daki Hasaiya Bayero a zamanin Sarki Ado Bayero, Sarkin duk da haka ya cigaba da hawan. Yakan fara daga Kofar Kwaru, Zuwa Unguwar Daneji, kusa da Mandawari. Daga nan sai ya ƙarasa Galadanchi, Diso, Ciranchi, Tudun Wuzirchi sai ya ƙarƙare a Kofar Kudu.

Shi kuwa Muhammad Sanusi II da ya zo, yakan yi wannan hawan ne zuwa gaida mai Babban Daki, Hajiya Saudatu. Mai Martaba ya na fitowa daga Kofar Kwaru, ya bi Kabara zuwa Tudun Wuzirci har ya isa Gwangwazo inda fadar ya ke.

Rana Ta Uku: Hawan Nassarawa

Sarkin Kano Abbas, wanda shi ne Sarkin farko da turawan mulkin mallaka su ka naɗa, shi ya fara wannan hawan. Ana yin hawan Nasarawa ne a rana ta biyu bayan hawan sallah a Kano, wato rana ta uku kennan.

Sarki yakan baro fadarsa ne kafin karfe takwas na safe tare da tawagarsa, ƙarƙashin jagorancin Makaman Kano. Mai Martaba zai wuce ta Wudilawa, Kankarofi zuwa Kofar Nassarawa inda zai tsaya a fadar Nasarawa domin yin addu’a ga kakanninsa; Sarkin Kano Abbas (Maje Nassarawa), Sarkin Kano Alhaji
Abdullahi Bayero, Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Inuwa, Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammad Sanusi da Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Bayan Sarki ya kammala, sai ya wuce Gidan Gwamnati inda Shugaban ƙaramar hukumar Tarauni da Hakimin Taraunin za su tarbe shi zuwa Africa House, inda Gwamna da tawagarsa ke jira.

Babban maƙasudin hawan Nasarawan dama shi ne domin kai ziyara ga Gwamna da muƙarrabansa. A nan duka Hakimai za su kai gaisuwa ga Mai Martaba, bayan nan shi kuma zai yi nasa jawabin, kafin Gwamna ya maida nasa martanin.

Sarkin Kano Hawan Nasarawa
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II tare da Gwamna Abdullahi Ganduje lokacin da Mai Martaban ya kai ziyara gidan gwamnati a Hawan Nasarawan shekarar 2017. Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Bayan an kammala, Mai Martaba zai bar Africa House zuwa Sabon Gari, inda talakawansa za su gaishe shi. Daga nan Sarki zai wuce Fagge, kafin ya wuce Ƙofar Mata. Kafin Azahar, Sarki zai ƙarasa ƙofar Fatalwa da ke arewancin fadarsa.

Rana ta Ƙarshe: Hawan Ɗorayi

Hawan Ɗorayi shi ne hawa na ƙarshe a jerangiyan Hawan sallah a Kano. Sarki na yi wannan hawa ne domin samun karɓar gaisuwan talakawansa da ke yammacin Kanon.

Mai Martaba ya na fitowa ne daga Kofar Kwaru da sassafe shi da tawagarsa, su wuce Daneji, Mandawari, Dandago, Sani Mainagge har zuwa Kofar Famfo. A Kofar Famfon ne Mai Martaba zai tsaya har sai bayan la’asar sai ya wuce Goron Dutse, Bakin Ruwa, Jakara, Tudun Nufawa, Makwarari, Sheshe ya ƙ a Soron Dinki, inda zai tsaya a Gidan Shatima su yi bankwana da Hakimi. Daga bisani, shi kuma sai ya wuce Kofar Kwaru.

Sarkin Kano a Hawan Dorayi
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a fadar Dorayi lokacin hawan 2017. Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Kafin Sarki ya sauka, ya na karɓar gaisuwa daga Sarakan Sullubawan Dabo a ɓangare ɗaya, da kuma sauran Sarakai a ɗayan gefen. Mai Martaba zai zo ya wuce ta tsakiya, ya shige fada, a inda hakan zai ƙarƙare hawan sallah a kano a wannan shekaran.

Hawan Fanisau

Ana Hawan Fanisau ne a rana ta huɗu na sallar layya.

Shirin Hawan Sallah A Kano

Ana fara shirin hawan sallah a Kano yayin da aka ce an ga watan Shawwal ko kuma ran goma ga watan Dhu al-Hijjah.

Ana idar da sallar asuba, ƙarar bindigu za su fara tashi.

Kafin nan dai dama Sarakai, Hakimai, Hadiman Sarki, da ma mutanen gari duk sun gama shiri. Ana cewa ranan idi ta yi, kowa zai yi shiri ya yi wanka ya yi ado. Mata da maza duka su na fitowa, kaman yadda shari’ar musulunci ta tanada.

Kayan Sarkin Kano

Sarkin Kano na saka kayan yaƙi da amawali, ko kuma ya sanya farar alkyabba na musamman. Bayan haka zai saka rawani da ke rufe da hular alkyabba, sannan kuma ya riƙe sandar girma. Takalmansa kuwa, an yi su ne da gashin dawisu.

Kwalliyan Sarkin Kano ranar sallah
Kwalliyan Sarkin Kano ranar sallah Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Hakazalika ba a bar taguwa ko dokin Mai martaba ba, domin su ma za a ƙawata su da kayan kwalliya na alfarma, sannan a bi da lema ta musamman.

Tawagar Sarkin Kano Ranar Hawan Sallah

Tawagar Sarki ta na ƙunshe da mutane iri-iri. Ga wasu daga ciki:

Masu Kakaki

Misali, a tawagar, akwai ‘yan kakaki wanda su ke sanar da cewa Sarki ya gabato. Ba wanda ake yi ma kakaki kaf masarutar, sai shi kadai.

Masu kakaki na Sarkin Kano
Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Ga wasu daga cikin ire-iren sautukan kakakin da ake yi ma Sarkin a hawan sallah a Kano:

  • Shafi bisa
  • Gangare
  • Rauni bisa rama
  • Ba sake ba manko aminci yafi ga linzami

‘Yan Bindiga

‘Yan bindiga su ma su na sanar da isowar Sarki wuri. Tun bayan sallan asuba za su fara aiki, su na tunatar da mahaya su fara shiri.

Idan Sarki ya fito daga fada, za a ji ƙaran bindiga, hakazalika idan ya zo Kofar Nasarawa, in ya iso gidan gwamnati, da kuma idan ya dawo fada.

‘Yan Algaita

Duk da cewa ana ma wasu Sarakai busan algaita, na San Kano ya banbanta.

Misali, daya daga cikin bushin algaitan da ake ma Sarkin shi ne in mai laifi bai fa sa ba mai horo ba zai dai na ba.

Yan algaita a hawan sallah a Kano
Yan algaita a hawan sallah a Kano Photo Credit: Ibrahim Ado-Kurawa

Sauran ‘yan tawagan Sarkin sun haɗa da makaɗa, ‘yan ƙaho, ‘yantambura, ‘yan tauri, sarkin yaƙi da jama’arsa, maharba, ‘yan baka da garaya, ‘yan kalangu, sarkin aska, ‘yan lifidi, da dai sauransu.

Tasirin Hawan Sallah A Kano

Sallolin idi na ƙarama da babba su ne manyan bukukuwan da ake da su a musulunci, dan haka su ke da tasiri a ƙasar Hausa musamman ma a Kano. Don haka ne mazauna garin su ke yin ado da kwalliya domin zuwa kallon hawan sallah a Kano.

Hasali ma, duk sallar da a yi hawa ba kamar yadda aka soke hawan sallan lokacin cutar Korona, gani ake yi ba ta cika ba. Hawan sallah na ƙara ma shagalin salla armashi.

Har’ila yau, hawan sallan na nuna ƙarfin da ƙasa take da shi da kuma jama’a. Wannan na da matuƙar amfani a zamanin da, da ƙasashen Hausan su ke yaƙe-yaƙe tsakaninsu. A yanzu kuwa sai dai a ce hawan sallan a Kano, wanda shi ne hawa mafi girma da ƙayatarwa a kaf fadin duniya, ya na kawo ma jihar kuɗin shiga ta hanyar masu zuwa yawon bude ido.

Cikin manyan maƙasudan yin hawan sallah a Kano, shi ne Mai Martaba ya samu daman ganawa da karɓar gaisuwa daga talakawansa. Da yawa daga cikin mazauna garin, hawan sallan ita ce kaɗai damar da su ke da ita na ganin Sarkin. Dan haka ne ma yara, manya, da maza da mata su ke caɓa ado don zuwa kallon Sarkin da tawagarsa.

Abu na ƙarshe, hawan sallah a Kano abu ne mai tsohon tarihi, domin an fi shekara 500 ana yin sa.

Idan kun gamsu da wannan rubutun akan yadda hawan sallah a Kano ya ke, mu na fatan za ku yaɗa shi kuma ku cigaba da ziyartar shafinmu domin samun ƙayatattun labarai. Za ka iya barin mana saƙo a nan ƙasa idan ka na da wani ƙorafi, gyara ko ƙarin haske.

About Abdullahi Malumfashi

Abdullahi marubuci ne a harshen Hausa, da kuma turanci. Bayan nan kuma mafasarri ne mai aikin tarjama daga Hausa zuwa turancin, ko kuma turanci zuwa Hausa. Har ila yau, shi din masani ne akan kafofin sada zumunta na zamani da kuma kasuwancin yanan gizo.

View all posts by Abdullahi Malumfashi →

Leave a Reply