Yadda Ake Duba Jarabawar NECO

Yadda ake duba jarabawar NECO

Shin ko ka na cikin waɗanda su ka rubuta jarabawar NECO? Shin ko ka san yadda ake duba jarabawar NECO cikin sauƙi da wayarka? Albishirin ka. Idan ba ka sani ba, ga shi zan koya ma yadda za ka duba jarabawar NECO cikin sauƙi da wayarka, ka na kwance a ɗaki.

Yadda ake duba jarabawar NECO abu ne mai sauƙi, ba wahala cikinsa. A wannan rubutun zan fayyace dukkan hanyoyin da ake bi wajen duba Jarabawar NECO. Ku biyo ni.

Me Ake Buƙata Wajen Duba Jarabawar NECO?

Kafin ka san yadda ake duba jarabawar NECO, dole sai ka na da abubuwa kamar haka;

 1. Shekarar Jarabawar (Exam year)
 2. Nau’in Jarabawar (Exam type)
 3. Lambobin Jarabawar wato (Registration number)
 4. Lambobin duba Jarabawar wato (Token).

Idan ma ba ka da katin duba Jarabawar NECO, zan nuna ma ka yadda zaka sayi katin da bai wuce Naira 700 ba a yanar gizo, kuma ka duba Jarabawa na ka hankali kwance.

Yadda Ake Duba Jarabawar NECO

Bayan ka tanadi waɗannan bayanan, abin da ya rage kawai sai ka bi waɗannan hanyoyin don sanin yadda ake duba Jarabawar NECO a yanar gizo;

1. Abu na farko shi ne, ka ziyarci shafin Hukumar Jarabawar NECO ta cikin burawza ta wayar ka a shafinsu na; https://result.neco.gov.ng/

2. Mataki na biyu shi ne ka zaɓi shekarar da ka yi jarabawar wato Exam year. Idan ka danna wajen, zai nuno ma ka Shekaru sai ka zaɓi shekarar da ka zana Jarabawar ta ka.

3. Mataki na gaba shi ne zaɓan Nau’in Jarabawar wato Exam type. Ka na dannawa zai nuna ma yadda za ake duba jarabawar NECO ta hanyar zaɓan kalar Jarabawar. Misali SSCE internal (Jun/Jul) ita ce wacce ake yi ta Gwamnati. Ita kuwa SSCE External (Nov/Dec) ga ɗaliban da su ke biya wacce ake kiranta da private NECO.

4. Mataki na huɗu shi ne ka sanya lambobin Katin duba Jarabawar NECO ɗin naka (Token) da ke jikin katin.

5. Mataki na gaba shi ne sanya lambobin Jarabawarka (Registration number).

6. Daga nan sai ka danna wajen da aka madanni mai koren launi da aka sa ‘duba sakamako’ (Check result).

7. Dannawan ka ke da wuya, zai watso ma sakamakon Jarabawar ta NECO. Daga nan fa, sai girban abin da ka shuka.

Yadda Ake Duba Jarabawar NECO ta Hanyan Sayen Katin Dubawa

Waɗannan hanyoyi ne da za ka bi wajen duba Jarabawar NECO ta hanyar sayan katin duba Jarabawar a yanar gizo.

 1. Da farko, za ka ziyarci shafin sayar da katin duba Jarabawar NECO, duk akan wayarka.
 2. Ka sanya cikakken sunanka.
 3. Ka cike lambar waya.
 4. Ka saka lambar sirri
 5. Ka tabbatar da lambar sirri.
 6. Sai ka yi rajista.
 7. Kabi maɓallin tantancewa da aka tura ma ta asusun Imel.
 8. Sai ka dawo ka shiga shafin sayar da katin duba Jarabawar NECO, ka danna wajen saya.
 9. Ka sanya adadin katin da ka ke so ka saya, misali guda 5.
 10. Danna maɓallin biya.
 11. Ka tantance dukkan bayanan cikin akwatin.
 12. Sai ka danna wajen biya ta Remita.
 13. Ka danna wajen biyan kudi ta remita
 14. Sai ka zaɓi hanyar biyan kuɗin da ka ga ta dace da ra’ayinka, ko katin banki, ko kuma turawa kai tsaye zuwa asusun banki da dai sauransu.
 15. Shikenan ka sayo katin duba Jarabawar NECO, sai ka dawo ka bi matakan da da aka faɗa a farkon rubutunmu domin ganin yadda ake duba jarabawar ta NECO. Da fatan Allah ya bada sa’a da nasara.

Amfanin Jarabawar NECO

Hukumar Zana Jarabawar kammala Sakandire ta kasa wato (NECO), Hukuma ce ta kasar Nigeria wacce take da alhakin tsara Jarabawar ƙarshe ta kammala makarantun Sakandire a faɗin ƙasar.

Za ka iya amfani da Sakamakonka na NECO don samun gurbin karatu a Jami’o’i, kwalejin Fasaha, Kwalejin ilmi a faɗin Nigeria.

Rufewa

Shin ka gamsu da yadda ake duba jarabawar NECO ɗin, ko ka na da sauran tambayoyi? Za ka iya tambayanmu a nan ƙasa, kuma za mu amasa ma ka nan take.

Da fatan za ka yaɗa wannan rubutun zuwa ga sauran ‘yan uwa masu son sanin yadda ake duba jarabawar NECO, kuma za ka bibiyi sauran rubuce-rubucenmu a wannan shafin. Idan kai ma yadda ake duba jarabawar NECO ta yanar gizo ya burge ka, kai ma za ka iya karanta yadda ake buɗe website cikin sauƙi.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply