Yadda Ake Bude Youtube Channel Cikin Sauƙi

Yadda ake bude Youtube channel

Shin ka kasance ka na sha’awar yadda shafin kallon bidiyo na Yotube ya ke aiki? Ko kuwa kai ma’abocin kallan bidyo ne a manhajan Youtube, kuma kai ma ka na so ka buɗe Youtube Channel na kan ka? To lallai ka ci sa’a, domin kuwa zan yi maka bayani dalla dalla akan yadda ake bude youtube channel, har zuwa matakin da za ka fara samun kuɗi.

Buɗe tashar Youtube abu ne mai sauƙi, kamar yadda ake bude website, ko ma in ce ya fi shi sauƙi. Domin kuwa a cikin daƙiƙa biyar ma za ka iya ƙirƙiran Youtube Channel cikin sauƙi da kuma muhimman bayanai ga wanda ke son bude youtube channel.

Idan ba ka san menene YouTube Chanel ba, to wata tasha ce a kan YouTube da za ka iya ɗaura bidiyo har kuma ka samu kuɗi da su, idan har ka cika wasu sharuɗa. Kafin nan dai, ga yadda ake bude Youtube Channel.

Yadda Ake Bude Youtube Channel

Matakan yadda ake bude youtube channel su na da yawa, kuma idan mutum ya bi su dalla-dalla, cikin ƙankanin lokaci zai kammala har ya fara kwasar dalolinsa cikin sauƙi.

Ga matakan da ake bi wajen bude youtube channel kamar haka;

1. Abu na farko da za ka fara yi shi ne za ka shiga cikin burauzar wayarka ko kwamfuta ka shiga shafin Youtube. Daga nan za ka ga wurin da aka sa ‘SIGN IN’ kamar haka, sai ka danna.

Yadda ake bude Youtube Channel

2. Daga nan sai ka danna ‘SIGN IN’ bayan nan zai buɗe ma ka in da za ka saka Gmail Account ɗinka. Idan kuma ba ka da shi, daga ƙasa za sai ka danna wurin ‘Create account‘ wato ƙirƙira sabon akawun.

3. Bayan akawun Gmail ɗin ka ya buɗe, daga sama sai ka danna da’ira mai ɗauke da harafin farko na sunan da ke kan Gmail Account ɗinka. Daga gefensa za ka ga an sa ‘Create a Channel’ sai ka danna.

4. Bayan ka danna ‘Create Channel’ zai buɗe ma ka wani shafi.

5. Daga nan sai ka zaɓi sunan da ka ke so a matsayin sunan channel ɗin ka.

6. Daga nan sai ka sake danna wurin da ke da harafin sunan ka a can gefen dama a sama, ka shiga ‘Your Channel.’

Yadda ake bude youtube channel

7. Bayan nan, sai ka danna ‘customize channel’ wanda zai kai ka wani shafin.

Yadda ake bude tashar Youtube

8. A nan za ka ga abubuwa uku kaman haka. Za ka iya shiga ‘Branding’, a in da za ka iya ɗaura hoton ka da na lagon tashan na ka, da kuma abin nuna alaman tashan na ka, wato Watermark.

Yadda ake kirkirar Youtube video

9. A ‘Basic info’ kuwa, za ka saka sunan mai tashan, da sunan tashan a wurin ‘handle’, sai kuma bayanin abin da tashan ta ƙumsa a ‘description’. Sauran bayanan da za ka iya ƙarawa sun haɗa da imel ɗin ka, ganin adireshin tashan na ka, da dai sauransu.

10. Bayan ka gama duk canje-canjen nan, sai ka dawo wurin ‘content’ a gefen hannun hagunka, ka danna wurin da aka saka ‘upload videos’ domin ɗaura bidiyo. Shikenan kai ma ka zama cikakken mai tashar Youtube.

Yadd Ake Samun Mabiya a Youtube Channel

Bayan ka gama sanin yadda ake buɗe Youtube channel, abin da ya rage sai ɗaura bidiyoyi da kuma samun mabiya.

Kafin ka samu mabiya a tashar YouTube, dole ka ɗaura bidiyon da zai burge masu kallo. Hakan kuma ba zai yiyu ba, sai ka san yadda ake gyara bidiyo, ayi tsabtace shi, kuma ya zama mai inganci mara batsa ko kalaman iskanci a ciki.

Daga nan za ka iya neman masu kallo da su danna ma ka ‘subscribe’ idan sun gama kallo, kuma sa yaɗa shi a shafukan zumunta, kai ma kuma ka yi haka.

Amfanin Bude Youtube Channel

Za ka iya tambaya, wai shin menene fa’idar sanin yadda ake bude Youtube channel? To wasu fa’idojin bude Youtube channel;

Samun Mabiya

Ɗaya daga cikin amfanin buɗe Youtube channel shi ne za ka samu mabiya, musamman idan harkan da ka ke yi na buƙatar samun mutane da yawa. Hakan zai taimaka ma ka wajen yin talla, da kuma samun kuɗi a Youtube ɗin.

Inganta Alaƙa da Masoya

Idan har kai mashahuri ne duniya mai ɗimbin masoya, to sanin yadda ake bude Youtube Channel zai taimaka ma ka wajen ƙara kusanci da masoyan na ka.

Hanyar Samun Kuɗi

Kamar yadda na faɗa a farkon rubutun nan, ana iya samun kuɗi ta hanyar buɗe tashar Youtube, idan har an cika wasu sharuɗa da su ka haɗa da samun mabiya aƙalla dubu ɗaya, kula da dokokin Youtube wajen ɗaura bidiyo da dai sauransu.

Za a iya samun daloli duk wata ta Youtube, zuwa asusun bankinka na dala nan take.

Kammalawa

Yanzu tun da ka kammala sanin yadda ake bude youtube channel, abin da kawai ya rage shi ne ka aiwatar a zahiri domin cin moriyar hakan.

Bude Youtube channel na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake samun maƙudan kuɗaɗe a yanar gizo, don haka kar ka yi ƙasa a gwuiwa.

Idan har ka na da sauran tambayoyi, za ka iya yin su a nan ƙasa, kuma za mu amsa ma daidai gwargwado. Mu na fatan za ka yaɗa wannan rubutun domin wasu su amfana.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply