Idan ka na so ka san yadda ake bude website, to ka zo inda za a share ma kuka. A zamanin yanzu bude website ya zama abu mai saukin gaske, musamman idan aka yi la’akari da yanayin cigaba da aka samu a bangaren fasaha.
Tabbas idan ka na da shafin saye da sayarwa a intanet ko kuma ka na harkan kasuwanci ko wata sana’a a intanet, ka na bukatar ka san ya ake bude website. Da website ne za ka tallata hajar ka, kuma ka samu kasuwa ba tare da kashe wani kudi mai yawa ba.
To amma fa idan ba ka san yadda ake bude website din ba, wato shafin yanar gizo, abin akwai dan sarkakiya. Saboda haka ne aka yi wannan rubutun, domin a fayyace maka yadda ake bude website cikin sauki, kai ma ya zama ka mallaki naka.
Yadda Ake Bude Website Dalla-dalla
1. Zabi Manhaja
Shafi bai samuwa sai da manhajar da ake gina shi, wato (platform). Akwai ire-irensu da yawa a duniya. Ga misalai;
- WordPress: https://wordpress.com/
- Wix: https://www.wix.com/
- Squarespace: https://www.squarespace.com/
- Shopify: https://www.shopify.com/
Kowanne a cikinsu na da na shi amfanin da kuma rashin amfanin, don haka ya na da kyau ka yi naka binciken akan su kafin ka yi zabinka. Amma in da zan ba ka shawara, sai in ce ka dauki WordPress, domin ya yi kaurin suna kuma bincike ya nuna cewa kaso fiye da 60 na duka shafukan yanan gizo su na amfani da manhajar WordPress ne.
2. Zabi Sunan Shafi
Sunan shafi wato domain na da matukar muhimmanci, domin duk wani mai son ya shigo shafin naka sunan da zai yi amfani da shi kenan.
Za ka iya sayan sunan a shafuka kamar haka;
- Namecheap: https://www.namecheap.com/
- GoDaddy: https://www.godaddy.com/
- Bluehost: https://www.bluehost.com/domains
- HostGator: https://www.hostgator.com/domains
- Domain.com: https://www.domain.com/
- Google Domains: https://domains.google/
- 1&1 IONOS: https://www.ionos.com/domains/domain-names
Kaman dai manhajan gina shafin, su ma su na da matukar yawa kuma kowanne da na shi tagomashin. Ni ina ba ka shawaran ka yi amfani da biyun farko, wato Namecheap da kuma GoDaddy domin samun dacewa da yadda ake bude website cikin sauki.
Da zarar ka biya kudin hayan shafin naka a daya daga wadannan shafuka, za a mallaka ma ka daman amfani da sunan shafin na tsawon shekara guda.
Kudin da za ka biya yawanci daga $5 zuwa $20, wato kaman a ce daga kwatankwacin dubu uku da dari biyar (3500) kenan zuwa dubu sha biyar (15,000) a lissafin Naira.
3. Zaban Kamfani mai Hada ka Da Yanar Gizo
Dole ne sai shafin ka ya hadu da yanar gizo mutane za su iya ziyartarsa. Za ka iya yin haka ne ta amfani da abin da ake kira Hosting Providers, wato masu sada ka da yanar gizo.
Su wadannan kamfanonin su na amfani da manyan kundinan aje bayanan shafinka, wato server. Ka na bukatan ka yi rajista da daya daga cikin kamfonin da ake da su domin yin wannan. Wasu daga cikin kamfononin sun hada da;
- Bluehost – https://www.bluehost.com/
- SiteGround – https://www.siteground.com/
- HostGator – https://www.hostgator.com/
- DreamHost – https://www.dreamhost.com/
- InMotion Hosting – https://www.inmotionhosting.com/
- A2 Hosting – https://www.a2hosting.com/
- Hostinger – https://www.hostinger.com/
- GreenGeeks – https://www.greengeeks.com/
- Liquid Web – https://www.liquidweb.com/
- WP Engine – https://wpengine.com/
Za ka iya bincika su, ka ga tsare-tsaren kowanne da kuma yanayin farashin na su kafin ka fara amfani da su. Farashin dai yawanci bai wuce $100 zuwa $150 a shekara.
Wasu abubuwan da ya kamata ka yi la’akari da su sun hada da ingancin kamfanin (trust and security), girman server din da za a ba ka (bandwidth), nauyi (RAM), sauri ko gudun sa (speed), kula da abokin hulda (customer support) da dai sauransu.
4. Zabi Manhajar Gina Shafi
Mataki na gaba a yadda za ka bude website shi ne zabar manhajar gina shafi. Manhajojin sun hada da;
- Wix – https://www.wix.com/
- Squarespace – https://www.squarespace.com/
- Weebly – https://www.weebly.com/
- WordPress – https://wordpress.com/
- Shopify – https://www.shopify.com/
Za ka iya amfani da wadannan domin ganin yadda ake bude website da zai ja hankalin masu karatu da duka wadannan, wadanda yawancin su kyauta ne.

Har ila yau, zan ba ka shawaran ka yi amfani da WordPress, sai dai fa idan shafin cinikayya ka ke son ka gina, sai in ce to ka yi amfani da shopify. Idan ka shiga, akwai ginannun shafukan da aka riga aka gina, kurum kai zaban wanda ka ke so za ka yi ka fara amfani da shi.
Ka na zaba, za ka iya gyara shafin na ka, ka canja kalan rubutu, tsari, da fasalin shafin naka yanda ka ke so.
5. Fara Wallafa Bayananka
Mataki na gaba a tsarin yadda ake bude shafi shi ne, ka fara wallafa rubutu, bidiyo, kayan da za ka saida ko hotuna a shafin naka.
Ka tabbata duk abinda za ka wallafa, ya kasance mai kayatarwa da burgewa yanda idan wani ya bincika abin da ya ke son samun bayani a Google zai iya cin karo da kai.
Sunan yanda ake hakan Search Engine Optimization wato yadda ake tsara bayanai domin Google su ji dadin nuna ma mai bincike a yanan gizo. Wannan shi ma rubutu ne na shi na musamman.
Ka na gama wannan, to fa ka kammalla aiki, sai wallafa. Kawai dai ya kamata ka tsaya ka tabbatar da komai na aiki yanda ya kamata kafin ka cigaba da amfani da shafinka.
A Takaice…
Yadda ake bude website dai abu ne mai sauki, domin za ka iya gama duka wadannan a cikin awa daya zuwa biyu kacal. Kawai dai bayan ka bude, ka na bukatan ka sa hakuri da jajurcewa domin ka cigaba da amfani da shi, ko don neman kudi ko kuma wani aiki daban.
Idan ka bi wadannan matakan da na lissafo na ya ake bude website, na tabbata za ka bude naka cikin ruwan sanyi ba tare da ka sha wata wahala ba. Idan kuwa ka fuskanci wata matsala, to za ka iya tuntubar mu a nan, domin mu na da kwararru da za su yi ma jagora tun daga farko har karshe.
Idan ka ji dadin rubutun nan na yadda ake bude website, kar ka manta ka yi mana godiya a kasa, ko kuma gyara idan mun yi wani kuskure.
Mun gode.