Yadda ake Bude Paypal Account

yadda ake bude paypal account

Shin ka san yadda ake yadda ake bude paypal account kuwa? Idan har ba ka sani ba, to zan yi ma bayani a wannan rubutun dalla-dalla akan yadda ake bude Paypal account. Paypal dai wani asusun yanan gizo ne wato e-payment plaform da a ke karɓa ko aike kuɗi ko ina a faɗin duniya.

Sai dai kafin mu shiga rubutun gadan-gadan, wani hanzari ba gudu ba. Ga masu san sanin yadda ake bude Paypal account a Nigeria, su sani cewa tun lokacin da Paypal ya zo Najeriya a shekarar 2014, ba a iya karɓan kuɗi daga wani wuri, sai dai aikewa kawai. Hakan kuwa na da nasaba da dokokin Paypal ɗin na rashin yin cikakken aiki a ƙasashe irin su Najeriya, Rasha, Sin da dai sauransu.

Amma fa hakan ba wai ya na nufin Paypal ɗin bai da amfani ba ne kwata-kwata, domin da kuwa haka ne ba amfanin wannan maƙalar. Za ka iya amfani da PayPal wajen tura kuɗi wasu ƙasashe, yin sayayya, biyan kuɗin wasu manhajoji kaman su Netflix da dai sauransu.

Idan kuwa har kai ma’abocin waɗannan ne, sai mu ce Bismil Lah, ga yadda ake bude Paypal account cikin sauƙi.

Yadda Ake Bude Paypal Account

1. Abu na farko da za ka yi wajen bude Paypal Account shi ne ziyartar shafin Paypal.

2. Daga nan sai ka danna wurin ‘Sign up’ kamar yadda ka gani a ƙasa don yin rajista.

Yadda ake bude paypal account

3. A shafin zai nuna ma ko ‘individual account’ wato na ka na kan ka, ko kuma ‘business account’ wato na kasuwanci kenan ko na kamfani. A ƙasa, sai ka danna ‘next’ wato cigaba kenan, bayan ka zaɓi wanda ka ke so.

4. Daga nan za ka cike ƙasan da ka ke da zama kamar haka.

5. Daga nan fa sai ka cike lambar da ka ke amfani da ita. Ka tabbatar ka cike lambar da za ka iya karɓan saƙon ‘OTP.’

5. Bayan nan sai ka cike bayanan imel, sunan farko da na biyu, sannan kuma ka zaɓi lambar sirri da ta ƙunshi harafi, lamba, alaman rubutu ko kuma wata alama.

6. A shafin gaba kuwa, a nan ne za ka cike adireshin ka na gida, gari da kuma lambar ofishin aika saƙo. Ka tabbatar ka yi amfani da lambar gidan da ka ke, ba wai na ofishin tura saƙo ba.

Ka na cike wannan ka kuma amince da tsare-tsaren Paypal na gudanarwa, shikenan ka mallaki asusun Paypal. Abin da ya rage kawai shi ne ka haɗa shi da katin bankin ka a nan take, ko kuma in ka so ka bari daga baya.

Ga yadda asusun na ka zai kasance a shafin Paypal na kwamfuta. Idan kuwa ka so, za ka iya garzayawa shafin Google na sauke manhaja domin amfani da manhajan na Paypal.

Abu na ƙarshe bayan sanin yadda ake bude PayPal account shi ne ka tabbatar ka kiyaye lamban sirrin ka, domin kuwa sai da shi za ka iya shiga asusun ka. Kar ka kuskura ka ba wani wannan lambar, domin kuwa za a iya ma ku kutse a kwashe ƴan kuɗaɗen ka.

Menene Fa’idan Amfani da PayPal?

Kamar dai yadda a ka faɗa a baya, PayPal tsarin kuɗi ne yanar gizo da ka iya karɓa kuma ka aike da kuɗi nan take cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

PayPal na PayPal tsarin biyan kuɗi ne na lantarki wanda ke bawa mutane damar aikawa ko karɓar kuɗi cikin sauki ta wayarku. PayPal na ɗaya daga cikin waɗanda su ka assasa biyan kuɗii ta yanar gizo, kuma an kafa shi ne a shekaran 1998, in da attajiri kuma mamallakin Twitter, Elon Musk shi da wasu mutane su ka jagoranta.

A halin yanzu, PayPal shi ne babban asusun tura kuɗi a faɗin duniya domin kuwa sama da mutane miliyan ɗari ke amfani da asusun wajen karɓa da kuma tura kuɗi a kan Intanet.

Wannan tsarin biyan kuɗi ya na ba mutane damar kammala ma’amala ta kan intanet ba tare da bayyana wani bayanin sirri, kamar lambobin katin kuɗi ko bayanan asusun banki ba. Wannan ne ma ya sa ma su harkan kirifto da sauran ire-iren su a yanan gizo ke jin daɗin amfani da shi.

Hakanan kuma kamfani ya na ba da walat ɗin dijital don adana kuɗi da biyan kaya da ayyuka a kan intanet. Hasali ma har biyan kuɗin website za ka iya yi da shi, idan ka tashi bude website.

Bayan PayPal Sai Me?

Za ka iya cewa bayan Paypal, wani hanyan kuɗi zan iya amfani da shi, musamman idan a ka yi la’akari da rashin iya karɓa kuɗi ta tsarin. To mu kuma sai mu ce ma akwai su Payoneer, Wise, Binance, Alipay wanda kamfanin China ne, Zelle, Apple Pay, da ma Binance.

Waɗannan a Ƙetare kenan. Idan a ka dawo gida Najeriya kuwa, sai mu ce su Opay, PalmPay, Moniepoint, Chipper Cash, Flutterwave, Paga, Paystack, Interswitch, da Kuda su ne kan gaba.

Wanne a cikin su ka ke amfani da shi? Za ka iya gaya mana a ƙasa.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply