Yadda Ake Bude Email

Yadda ake bude sabon email

Shin ka san amfanin email kuwa? Ka ma san yadda ake bude email? Idan har ba ka sani ba, to lallai an baro ka a baya, domin kuwa mafi akasarin abubuwa a yanan gizo yanzu sai da email. A wannan ƙarni na 21 da mu ke ciki kuwa, tabbas yanar gizo na taka muhimmin rawa a rayuwar mu, ko a ma ce dole sai dai yanar gizon rayuwa za ta gudana.

To amma dai ko ba ka san yadda ake bude email ba babu damuwa, domin kuwa zan fayyace ma ka yadda za ka bude sabon adireshin emial dalla dalla.

Matakan Bude Sabon Email

Yadda kowane abu ke da matakai, haka ma bude sabon email ke da matakai. Ga bayanin a tafe;

1. Za ka buɗe browser din ka, sai ka shiga shafin gmail.

2. Bayan ka ziyarci wannan shafin, za ka ga in da aka rubuta “create new account” a sama, sai ka danna.

3. Daga nan zai kai ka shafin da za ka cike sunan ka da na mahaifinka, wanda ba dole ba ne.

Yadda ake bude email

4. Bayan haka sai ka saka ranar haihuwan ka da kuma jinsin ka, wato mace ko namiji.

5. Ka na gama wannan, za su nuno ma zaɓin email da a ka yi amfani da sunan da ka cike. Idan ka so, sai ka zaɓi wanda su ka ba ka, idan kuwa ka ga ga dama, sai ka danna ‘create your own gmail address’ domin ƙirƙiran na ka.

6. Idan har wani bai yi amfani da wanda ka saka ba, to zai kai ka shafin da za ka zaɓi lambar sirri. Wannan lambar sirrrin wajibi ne ta ƙunshi harafi, lamba, da kuma alama guda ɗaya.

Yadda ake bude sabon email

7. Domin tabbatar da cewa kai ba mutum-mutumi ba ne, za ka sa lambar wayar ka daga bisani a turo ma ka saƙon lambobi wanda za ka saka kamar haka.

8. Daga nan sai ka aminta da tsare-tsaren Google ka kuma yadda da ƙa’idojin su.

9. Shikenan ka kamalla bude sabon email, abin da ya rage kawai sai ka ziyarci shafin gmail ko ka sauke manhajarsu domin tura saƙo da kuma amsa. Sauran abubuwan da su ka rage, za ka tadda su a cikin saƙon email da za su turo ma a sabon email ɗin na ka.

Za kuma ka iya bin waɗannan matakan domin buɗe sabon email a wani wurin kaman su Yahoo mail, ko kuma hotmail.

Meyasa Ya Kamata In Mallaki Email?

Email wata fasaha ce, wacce aka kirkireta don taimakawa mutane akan tafiyar da al’amuransu na yau da kullum na yanar gizo. Idan ka na son buɗe kafan sada zumunta kaman su Facebook ko Instagram, ko kuma bude Youtube channel, to lallai kuwa ka na buƙatan ka san yadda ake bude email, domin kuwa sai da shi.

Hakazalika, wurin wasu sabgogin kaman su bude paypal account domin tura turawa da karɓan kuɗi ta yanan gizo. Hasali ma dai, har lambobin wayanka za ka iya ajewa kan Email.

A na kuma amfani da email ne musamman a wajen aiki, domin karɓa da aike saƙonni da su ka shafi aikin, ko kuma ma neman aikin, wajen cike jarabawa irinsu NECO, harkan karatu da dai sauransu.

Nau’oin Email

Kamar yadda na bayyana a baya, akwai ire-iren email da damma, irinsu Gmail, hotmail, yahoo mail da dai sauransu.

A cikinsu kuwa, wanda ya fi kowanne suna a duniya shi ne Gmail, domin ya fi su sauƙin amfani, tsaro, kuma mallakin Google ne da su ka mamaye ko ina.

Za kuma ka iya amfani da shi a duka sauran tsare-tsaren Google, kamar su Google Play Store na sauke manhaja a wayarka, Google Maps, Google Drive, Google Photos, Contacts, da dai sauransu.

Kammalawa

Sanin Yadda ake bude email na da amfani sosai duba da yadda adireshin email ke da amfani a yau. Za mu iya cewa, dole sai da adireshin email za ku ci moriyan yanar gizo yadda ya kamata.

Don haka ne ma sanin yadda ake bude sabon email ke da amfani matuƙa. Dalilin haka ne ma ya sa na rubuta wannan ƴar maƙalar a kan yadda ake bude email domin ku amfana.

Shin ka fuskanci wani ƙalubale yayin bude sabon email ɗin? Ko kuwa ka maƙale a wani wuri? Za ka iya aje bayanin abin da ka fuskanta domin in taya ka shawo kan lamarin.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply