Yadda Ake Bude BVN Number

Yadda ake bude bvn number

Idan har ka na san buɗe asusu a banki, dole ne a buƙaci BVN. Idan kuwa ba ka da shi, dole ka tambayi yadda ake bude BVN number. Samun bunƙasar  fasahar zamani shi ke haifar da hada-hadar kuɗade. Hakan ya sa masu damfara da zamba su ka yawaita. Dalilin haka ne ya sa Babban Bankin Najeriya ya fito da tsarin BVN number, domin tantance masu hada-hadan kuɗi na gaske.

Lokacin da aka fito da tsarin BVN mutane da dama sun ji tsoro, da fargabar dole sai mutum ya je banki ya bi layi sannan a iya yi. Amma yanzu kam abu ya canja, domin kam mutum zai iya yi daga ɗakinsa. TKa na san sanin yadda ake buɗe BVN number? Biyo mu.

Abubuwan Da Ka Ke Buƙata Wajen Bude BVN

Kafin sanin yadda ake bude BVN number, abubuwa da ake buƙata su ne kamar haka:

  1. Shaidar katin ɗan ƙasa ko katin fasfo, ko katin tuƙi
  2. Hoto guda ɗaya
  3. Fam na cika bayanai

Yadda Ake Bude BVN Number

Idan ka na san sanin yadda za ka bude BVN a yanar gizo, to ga matakan da za ka bi;

Wadannan sune hanyoyin da zakabi ka bude BVN da kanka kana zaune; Amma Dole bayan ka cike bayananka a online saikaje centre don karasa ma

1. Bayan ka hau kan burausar wayar, sai ka ziyarci shafin da ka cike bayanan BVN ɗin ka.

2. Za ka cike bayanan BVN ɗin ka, sai ka sanya ranar da za ka je domin a shigar da yatsan ka.

3. A ranar dole ka kai kanka wajen rajista, da dukkanin bayananka tare da katin shaidan ranar.

4. A nan za ka samu wanda zai ƙarasa.

Yaushe Zan Iya Fara Amfani da BVN Ɗi Na?

Bayan an gama saita ma BVN, za ka ɗauki tsawon kwana guda kafin a turoma da lambar BVN ɗinka.

Menene BVN?

BVN Bank verification number wasu lambobi ne guda goma sha ɗaya (11), waɗanda su ke na musamman kuma ba mai irinsu. BVN na na taimakawa sosai ga banki wajen sanin kwastomansu da kuma magance masu damfara.

Rufewa

Shin ka gamsu da yadda ake bude BVN number? Ko kuwa ka na buƙatan ƙarin taimako? Za ku ma ka iya karanta bayanin yadda ake bude website cikin sauƙi.

About Salim Khan

Salim Khan marubuci ne da harsunan Hausa da Ingilishi, kuma masani ne kan harkokin yanar gizo. Salim na kuma tofa albarkacin bakinsa akan harkokin siyasa, zamantakewa da rayuwa as shafukan sada zumunta.

View all posts by Salim Khan →

Leave a Reply