Sababbin Karin Magana na 2023

Sababbin karin magana

Karin magana wasu zantuka ne masu cike da hikima da iya zance da Malam Bahaushe ke shiryawa. Akwai ire-iren karin magana da dama, ciki har da waɗannan sababbin karin maganan.

Kula: Ba a yi wannan rubutun domin cin mutuncin wani ko ɓatanci ba, hasali ma an tattaro sababbin karin maganan ne daga zantukan mutane a yanan gizo.

Sababbin Karin Magana 2023

1. Duniya juyi juyi…El-Rufai da tausayin talakawa.

2. A faɗa a cika…Yahaya Bello da ƙwato ‘yancin masu albashi.

3. Abin mamaki…Ganduje da yaƙi da cin hanci da rashawa.

4. Zancen ka ke so, wai an ce ma Abduljabbar ina hujja.

5. Da sauran gyara, Buhari ya ga talaka da babbar waya.

6. Mun tuba mun bi Allah, ɗan APC ya zo neman ƙuri’a.

7. Akwai haske, dan PDP ya sha kaye

8. Taliya ba ta zaɓe, ɗan NNPP ya sha da ƙyar

9. Abun na Allah ne, talaka ya ci taliya mai tsada (‘Yar shekara 4)

10. Garin daɗi na nesa, ɓarawo ya hango akwatin zaɓe.

11. Ƙasa ta birkice, ba mu ga ta zama ba, takara ta kama mai goyo.

12. Rufe  mun border, Buhari ya ga talaka da tumbi.

12. Aikin banza, talaka na APC.

13. Aikin banza, a gama kashe kuɗi a akwati da dinner, a kai amarya gidan haya.

14. Gaba da gabanta, bestie ya yi arangama da late comer.

15. Ta nan muka fara, wai karuwa ta ga yar Tiktok.

16. Bar ganin ka yi Sahur, kiyayi bayan la’asar.

17. Rashin hankali, zagin Annabi (S.A.W) a Sokoto.

18. Ganganci, aje aikin ka shekara guda kafin zaɓe.

19. Samun matsayi, wai ɗan fashi da tuhumar malam da sata.

20. Ana murna Buhari ya tafi, ashe Bola na bayan gari.

21. Ta nan mu ka fara, wai karuwa ta ga yar Tiktok.

Wanne cikin sababbin karin maganan ya fi ƙayatar da kai? Kuma wani sabon karin magana za ka iya gaya? Rubuta a nan ƙasa.

Leave a Reply