Littattafan Hausa na Wattpad Guda 10

Littattafan Hausa Wattpad

Wattpad wata manhaja ne da ake karanta littattafai kyauta. Ana ziyartar shafin Wattpad na da masu amfani sama da miliyan 90 a wata, da kuma marubuta aƙalla 500,000. Ka ga kuwa gano littattafan Hausa Wattpad zai yi wuya idan aka yi la’akari da yawan littatafan. A dalilin haka ne aka rubuta wannan maƙalar domin bayyana manyan littattafan Hausa Wattpad, ciki har da  tsofaffin Hausa novels Wattpad.

Karanta: Yadda Ake Buɗe Website Cikin Sauƙi

Manyan Littattafan Hausa Wattpad

1. Matar Ƙabila

Suwaiba Muhammad ce marubuciyar wannan littafin da aka fara shi a watan Oktoban 2017 aka kuma kammala a watan Disamban shekaran.

A lokacin da aka wallafa rubutun nan a watan Yulin 2023, mutane dubu ɗari uku da talatin ne su ka karanta shi, tare da mutane dubu ashirin da bakwai da su ka saka littafin a cikin jerin llittattafan Hausa Wattpad da su ka fi so.

Karanta a nan

2. Zan So Ka A Haka

Wannan littafin Hausa Wattpad ɗin Queen BK ce ta wallafa shi a kammala a shekaran 2020. An shafe shekaru biyu cur a na rubuta wannan littafin, kuma mutane 363, 000 su ka karanta shi tare da mutane 22,734 su ka so shi.

Karanta a nan

3. Ba A Kan Ta Farau Ba

An rubuta wannan littafin Hausa Wattpad ɗin ne a shekaran 2018. Littafin, mai babi 37 Ummu Asgar ce ta rubuta shi, kuma ya samu karɓuwa har mutane 100,000 su ka karanta shi, da kuma masoya fiye da dubu bakwai. 

Karanta a nan

4. Mijina Ne!

Wannan na ɗaya daga cikin jerin zafafan llittattafan Hausa Wattpad da Aisha Malumfashi ta wallafa. Marubuciyar ta rubuta littatafai ashirin, ciki guda uku na Hausa.

Mijina ne ya samu karɓuwa wajen mutane 84,268 da su ka karanta shi duk da cewa ya na da babi har 55. An rubuta littafin ne lokacin cutar Korona, aka kuma kamalla duk a lokacin. Wannan ya na cikin jerin littafan Hausa Wattpad da na fi so.

Karanta a nan.

5. Rayuwar Badiya

Rayuwar Badariya litattafan hausa wattpad

Rayuwar Badiya ma na daga cikin llittattafan Hausa Wattpad da Aisha Malumfashi ta wallafa a shekaran 2020, duk da dai an fara shi ne a 2018. Mutane 235,866 ne su ka karanta shi a lokacin da ake wannan rubutun, kuma mutane dubu sha tara sun gamsu da shi.

Karanta a nan

6. Sooraj

Idan ka ji sunan wannan littafin, sai ka yi tunanin na Indiya ne, alhalin kuwa Fatyma Sardauna ce ta rubuta shi a shekaran 2020.

Mutane 762,000 ne su ka karanta shi, tare da mutane dubu sittin da bakwai da littafin ya burge su.

Karanta a nan

7. Al’amarin Zuci

Shararriyar marubuciyar Wattpad da Okadabooks, Azizah Idris Gombe wacce aka fi sani da Ummu Yasmeen ce ta rubuta wannan littafin. Marubuciyan ta rubuta wasu littatafan Wattpad da dama, sai dai kash ba da Hausa ba ne. Za ku iya duba sauran littatafanta a Wattpad kaman su Becoming Mrs Bugaje da Being Bilal’s Wife.

Abin da zai burge ka da wannan littafin shi ne an rubuta shi ne tun shekarar 2016 aka rubuta shi, amma har yanzu kaman sabo ya ke domin ya sosa ma in da ya ke ma mata da yawa ƙaiƙayi. Shiyasa ban yi mamaki ba da na ga mutane 261,048 sun karanta shi.

Kuma za ku iya karanta shi a nan. 

8. Maimoon

Maman Maimoon ta rubuta wannan littafin a shekarar 2018. Ya na daga cikin tsofaffin Hausa novels Wattpad da ya shara a da can baya, domin kuwa mutane sama da 679,605 su ka karanta shi. A cikinsu, mutane sama da dubu hamsin sun nuna amincewarsu ga littafin.

Littafin Maimoon na da ƙayatarwa cike da ban tausayi da soyayya, idan har kai ma’abocin littatafan Hausa na soyayya ne.

Za ku iya karantawa a nan.

9. Diyam

Tabbas yadda sunan Diyam ya ke da jan hankali, haka labarin ke da jan hankali. Diyam littafi ne mai cike da darussa da dama. Dole ne a yaba da ƙwazon Maman Maimoon da ta rubuta littafin a cikin watanni 4 kacal.

Mutane 844,524 da su ka karanta shi sun tabbatar da lallai ba saurin banza kawai ta yi ba.

Ku ma za ku iya karanta shi a nan.

10. Abdulkadir

Abdulkadir tosfaffin Hausa novels

Da ƙyar a ka zaƙulo wannan littafin cikin jerin littatafan Hausa Wattpad na marubuciyar, domin kuwa ta rubuta llittattafai kusan goma duka na Hausa kuma masu ƙayatarwa.

Mutane sama da 300,000 ne su ka karanta littafin nan, kuma 30,667 su ka aminta da shi. An kammala rubuta littafin soyayyan da kuma labarin sojojin ne a 2020.

Za ku iya karantawa a nan.

Rufewa

Akwai llittattafan Hausa Wattpad da dama, sai dai waɗannan su su ka fi shahara da tsaruwa. Shin wani littafin Hausa Wattpad ka fi so, sabo ko tsoho? Shin ka fi son na soyayya ne ko kuma na wani abu daban? Fa

Akwai llittattafan Hausa Wattpad da dama, sai dai waɗannan su su ka fi shahara da tsaruwa. Shin wani littafin Hausa Wattpad ka fi so, sabo ko tsoho? Shin ka fi son na soyayya ne ko kuma na wani abu daban? Faɗa ma na a nan ƙasa.

Idan kuma kai ma’abocin llittattafan turanci ne da aka rubuta shi a Arewa, to za ka iya karanta littatafai irinsu Being Bilal’s Wife, Becoming Mrs. Bugaje, Hilwa, From the Eyes of A Spinster, Alkyabba da dai sauransu.

About Aliyu Ahmed

Aliyu Ahmed marubuci ne, kuma masanin masanin kasuwancin yanan gizo wato Digital Marketing da kuma kula da shafukan sadarwan zamani wato Social Media Management.

View all posts by Aliyu Ahmed →

Leave a Reply