Karin Magana Guda 30

Karin magana guda 30

Idan dai kai bahaushe ne, ko kuma ka kasance ka na magana da yaren Hausa, to ba shakka ka taɓa cin karo da karin magana. A wannan maƙalar, zan tafi kai tsaye ne in lissafo karin magana guda 30 da ya kamata ka sani, da kuma ma’anarsu.

Domin samun ƙarin bayani game da karin magana, za ka iya karanta ma’anar karin magana da kuma ire-iren karin magana da a ka riga a ka yi bayanin su a baya.

Yanzu ta kai ga an cigaba har ma sababbin karin magana da karin magana na zamani duk akwai.

Idan kuwa ka gamsu, kai kawai karin magana guda 30 ka ke nema, sai mu ce ma ka kawo kukan ka in da za a share ma, domin kuwa ba karin magana guda 30 ɗin kawai mu ka kawo ba, hadda ma’anar su a turanci.

Me ka ke jira?

Karin Magana Guda 30

1. Bayan wuya sai daɗi.

Meaning: After every hardship comes ease.

2. Ba kullum a ke kwana a kan gado ba.

Meaning: No condition is permanent

3. Da ƙyar na sha, ya fi da ƙyar a ka kama ni.

Meaning: Beter late than never.

4. Gaskiya dokin ƙarfe.

Meaning: Honesty is the best policy.

5. In da rai, da rabo,

Meaning: Where there’s life, there’s hope.

6. Ilmi gishirin zaman duniya.

Meaning: Knowledge is power.

7. Kyawun ɗa, ya gaji uban sa.

Meaning: Like father, like son.

8. Mahakurci mawadaci.

Meaning: Patience is a virtue.

9. Girman kai rawanin tsiya.

Meaning: Pride comes before a fall.

10. Rashin sani ya fi dare duhu.

Meaning: Ignorance is bliss.

11. Sauri ya haifi nawa.

Meaning: Haste makes waste.

12. Da zafi-zafi akan bugi ƙarfe.

Meaning: Make hay while the sun shines

13. Ba a shan zuma sai an sha harbi.

Meaning: No pain no gain.

14. Ɗan uwa rabin jiki.

Meaning: Blood is thicker than water.

15. Haɗin kai shi ne ƙarfi.

Meaning: United we stand, divided we fall.

16. Yaro da rarrafe kan tashi.

Meaning: You must crawl before you walk.

17. Ido wa ka raina? Wanda na ke gani kullum.

Meaning: Absence makes the heart grow fonder.

18. In kunne ya ji, jiki ya tsira.

Meaning: A word is enough for the wise.

19. Komai nisan dare, gari zai waye.

Meaning: However long the night, the dawn will break. 

20. Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutu.

Meaning: Curiosity killed the cat.

21. Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi tsaki?

Meaning: Don’t count your chickens before they hatch.

22. Kowa da ranarsa.

Meaning: Every dog has its day.

23. Abincin wani guban wani.

Meaning: One man’s trash is another man’s treasure/ one man’s food another man’s poison.

24. Guntun gatarin ka ya fi sari ka ba ni.

Meaning: Half a loaf is better than none.

25. Abun da ka shuka, shi za ka girba.

Meaning: You reap what you sow.

26. Duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara.

Meaning: A leopard can never change its spot.

27. Laifin daɗi, ƙarewa.

Meaning: All good things must come to an end.

28. Ƙaramin sani, ƙuƙumi.

Meaning: A little knowledge is a dangerous thing.

29. Gida bai ƙoshi ba, ba a kai wa daji ba.

Meaning: Charity begins at home.

30. Gani ya kori ji.

Meaning: Seeing is believing.

Rufewa

Kamar yadda a ka sani, karin magana dai wani salon magana ne na isar da wani muhimmin saƙo da kalamai ƙalilan.

Karanta: Karin Magana Akan Gaskiya

An zaƙulo waɗannan karin magana guda 30 ne duba da muhimman saƙonnin da su ke ƙunshe da su, da kuma shaharar su.

Shin wanne cikin karin magana guda 30 ya fi burge ka? Ko kuma wannene ka ke ganin ma’anar ta ba ta dace ba?

Za ka iya faɗa mana a nan ƙasa.

About Aliyu Ahmed

Aliyu Ahmed marubuci ne, kuma masanin masanin kasuwancin yanan gizo wato Digital Marketing da kuma kula da shafukan sadarwan zamani wato Social Media Management.

View all posts by Aliyu Ahmed →

Leave a Reply