Karin Magana Akan Gaskiya Guda 15

Karin magana akan gaskiya

Shin akwai karin magana akan gaskiya na Hausa? Idan har akwai, wasu misalai ne su ka fi shahara? Karin Magana wasu kalamai ne da ke cike da Hausawa ke amfani da su wajen isar da saƙo cikin sauƙi. Karin Magana yawanci su na cike ne da hikima da basira, kuma gajeru ne.

Hasali ma, kamar yanda Farfesa Ɗangambo ya fada;

Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ƴan kalmomi kaɗan, cikin hikima.”

Farfesa Ɗangambo

Karin Maganan da ake da su a Hausa ba za su ƙirgu ba, sai dai akan iya kiyasi a ce sun fi dubu goma. A kowane fanni za ka samu akwai karin maganan da hausawa su ka yi. Akwai karin magana akan gaskiya, karin magana akan soyayya, karin magana akan lokaci, karin magana akan hassada, karin magana akan hakuri da dai sauransu.

A wannan maƙalar, za mu yi bayani ne akan karin magana akan gaskiya. Ba tare da bata lokaci ba, ga wasu ire iren karin maganan da ya kamata ku sani akan gaskiya.

Karin Magana Akan Gaskiya

  1. A dade ana yi sai gaskiya. Ma’ana: Gaskiya ita ce ke karo.
  2. Allah Ya hana kunya ranar gaskiya. Ma’ana: Ba a jin kunya wajen fadan gaskiya.
  3. Ciki da gaskiya wuka bata huda shi. Ma’ana: Mai gaskiya ba abin da zai same shi.
  4. Daki mai duhu, mara gaskiya ke tsoron shiga. Ma’ana: Mara gaskiya ne ke tsoron shiga hali mai wuya.
  5. Duniya ba gaskiya, barawo ya rasa shaida. Ma’ana: Ko mara gaskiya ya san amfaninta.
  6. Gaskiya ɗaci gare ta. Ma’ana: Wani lokacin, ba ta da daɗin faɗa.
  7. Gaskiya matakin nasara. Ma’ana: Da gaskiya ake cin nasara a rayuwa.
  8. Gaskiya ta fi tafin hannu cike da zuma. Ma’ana: Gaskiya ta fi abu mai dadi
  9. Gaskiya ta fi kwabo. Ma’ana: Gaskiya ta fi kudi
  10. Gaskiya dokin karfe, duk wanda ya hau ba zai yi nadama ba. Ma’ana: Dokin karfe in aka hau zama daram dam. Haka gaskiya ta ke.
  11. Komai daɗin karya, gaskiya ta fi ta. Ma’ana; Gaskiya ta fi karya daɗi
  12. Komai za ka faɗi, faɗi gaskiya komai ta ja maka ka biya. Ma’ana: Duk rintsi duk wuya, fadi gaskiya
  13. Mai cinikin karya, ya yi biyan gaskiya. Ma’ana: Duk ranar karya, amfanin gaskiya na nan zuwa.
  14. Mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi. Ma’ana: Mara gaskiya ko a halin natsuwa bai da sukuni
  15. Zato zunubi, ko da ya zamo gaskiya. Ma’ana: An kyamaci zato.

Wani karin Magana ku ka sani akan gaskiya? Ko wani karin Magana akan gaskiya ku ke buƙatan ƙarin bayani ko sharhi akai? Ku yi mana bayani a ƙasa.

About Aliyu Ahmed

Aliyu Ahmed marubuci ne, kuma masanin masanin kasuwancin yanan gizo wato Digital Marketing da kuma kula da shafukan sadarwan zamani wato Social Media Management.

View all posts by Aliyu Ahmed →

Leave a Reply