Ana Iya Shan Bagaruwa Kuwa? Ga Amsa Daga Masani

Ana iya shan bagaruwa

Idan kai mazaunin ƙasar Hausa ne, babu makawa cewa ka taɓa jin masu yawo da maganin gargajiya su na shela a lasifika game da amfanin shan bagaruwa. Shin da gaske ne akwai amfanin shan bagaruwa kuwa? Kuma idan ma akwai, shin ana iya shan bagaruwa? Ku biyo ni a wannan rubutun domin in fayyace maku gaskiyan lamarin.

Shin Ana Iya Shan Bagaruwa?

Tabbas ana iya shan bagaruwa, kuma wannan ba sabon abu ba ne a wajen Malam Bahaushe domin kuwa bagaruwa na da amfani sosai ga jiki, musamman ga budurwa.

An daɗe a na shan bagaruwa a matsayin maganin gargajiya wajen magance matsaloli da yawa.

Sau da yawa waɗansu masu siyar da maganin gargajiya su na danganta bagaruwa da maganin cututtuka dayawa, wanda a wani lokacin ma sukan wuce gona da iri.

Akwai nau'i na bagaruwa da ake amfani da shi wajen maganin ciwon hakori

Masana binciken ƙwayoyin halitta da itatuwa na Najeriya da ƙasashen waje sun yi bincike sosai game da amfanin shan bagaruwa, sannan da waɗansu illolinsa.

A na iya amfani da ganyen ko ƙwayoyin ko kuma sassaƙen bishiyan domin amfani kamar haka;

Amfanin Shan Bagaruwa

Shan Bagaruwa Na Rage Raɗadin ciwo

A na iya shan bagaruwa wajen maganin zafin ciwo, kumburin ciwo, waɗansu nau’oin ciwon ciki, da ciwon maƙogoro, hakazalika wajen magance ƙaiƙayi.

Amfanin shan bagaruwa ya biyo bayan waɗansu sinadarai da masana bincike su ka gano.

Bagaruwa Na Taimakawa Wajen Warkewar Ciwo

Masu bincike sun gano cewa haɗa baguruwa da waɗansu nau’o’in mai na shafawa zai iya gaggauta warkewar ciwo kamar su miki, gyambo da sauransu fiye da idan da ba a yi amfani da shi ba.

Inganta Tsabta da Lafiyar Hakori

A na iya shan bagaruwa domin magance ko kuma kiyaye waɗansu nau’o’in ciwon haƙori.

Hakan ya fi aiki ne idan a ka saka garin a cikin kayan haɗe-haɗen man goge baki (toothpaste).

Za a iya samun ire-iren su wanda a ka riga a ka haɗa tun a kamfani. Idan a ka yi amfani da shi, bagaruwa na taimakawa wajen cire dauɗa daga baki.

Bagaruwa Na Ƙunshe Da Sinadari na Fibre

Sinadari na fibre na da amfani wajen rage ƙiba ko teɓa, kare kai daga basir ko atine, da kuma rage yawan gurɓataccen mai na cholesterol daga jikin mutum, wanda yawan sa yakan iya kawo ciwon zuciya da toshewar magudanar jini.

Shan Bagaruwa Na Maganin Tari da Mura

Ana iya amfani da bagaruwa wajen maganin tari, mura, zafi da ƙaikayin maƙoshi.

Hakan ya kasance ne saboda ya na ƙunshe da sinadarai masu rage kumburi, zafi da ƙaikayi.

Idan ka taɓa rasa muryar ka a lokacin da ka ke mura, za ka iya shan bagaruwa domin hana maimaita aukuwar hakan.

Shin A Na Iya Fuskantar Wata Matsala Idan A Ka Sha Bagaruwa?

Kamar ko wani irin maganin Bature ko na gargajiya, a na iya fuskantar wani matsala (side effect) idan a ka sha ko, a ka shafa bagaruwa ko kuma a ka yi amfani da shi ta wani hanya na daban.

Waɗnan sun haɗa da zubewan gashi, hana jiki amfani da waɗansu sinadarai na cikin abinci, da kuma hana waɗansu magunguna na Bature aiki.

A bisa wannan dalilin ne ya zama bai kamata a sha bagaruwa ko ma wani maganin gargajiya a lokacin da a ke shan na asibiti.

A Taƙaice

A na iya shan bagaruwa domin magance matsaloli da dama, cikin su har da raɗaɗin ciwo da ciwon haƙori.

Amfanin shan bagaruwa kuwa sun haɗa da rage zubar jini, inganta lafiyan haƙori, maganin tari, ciwon ciki da waɗansu cututtukan ƙwayoyin Bakteriya.

Masana na nan na kan bincike game da amfanin shan bagaruwa, domin kuwa ba a gama gano amfaninsa da illolinsa ba, saboda haka ya na da kyau mutane su yi taka-tsantsan wajen shan bagaruwan, kuma kada su ƙi zuwa ganin likita ko kuma su ƙi shan maganin da a ka rubuta musu a asibiti saboda sun karanta wadannan amfanin shan bagaruwan.

Ya na da kyau a kodayaushe a tuntuɓi likita idan a na rashin lafiya.

About Abdulsalam Yunusa

Abdulsalam Yunusa ɗalibin ilmin likitanci ne da ke gab da kamalla karatun shi. Abdulsalam marubuci ya shafe fiye da shekaru uku ya na rubutu a kan kiwon lafiya da harshen Hausa da Ingilishi, tare da wayar ma mutane da kai akan lafiyarsu a dandalin Facebook. Har ila yau, Abdulsalam ƙwararre ne akan harkar zane-zane wato Garphics design, da kuma tarjama da fassara. Idan har ya samu lokaci, Abdulsalam na ɗan taɓa karance-karance.

View all posts by Abdulsalam Yunusa →

Leave a Reply